23 Oktoba 2024 - 07:30
Ana Ci Gaba Da Gudanar Da Taron Girmama Shahid Yahya Sinwar A Ofishin Hamas Da Ke Tehran

Abu Arif shugaban ofishin majalisar koli ta kasar Iraki a birnin Tehran ya halarci wajen taron tunawa da shahid Sinwar a ofishin wakilin Hamas da ke Tehran.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlul Bait (As) - ABNA - ya habarta cewa: A jiya ne aka fara gudanar da taron tunawa da shahid Sinwar shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a Gaza a ofishin kungiyar Hamas da ke birnin Tehran kuma yana ci gaba da gudana har zuwa yammacin yau.